‘Yan bindiga sun kashe maitamakin shugaban kungiyyar Izala a Kaduna

0 296

’Yan bindiga sun kashe manoma shida, cikinsu har da Mataimakin Shugaban kungiyar Izala na Karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna, Malam Yakubu Bugai.

Kazalika, rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kuma sace sama da mutum 40 lokacin da suke tsaka da aiki a gonakinsu a yankin mai fama da hare-hare.

Shugaban Kungiyar Ci Gaban Masarautar Birnin Gwari (BEPU), Ishaq Kasai ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya, inda ya ce an kai farmakin ne ranar Larabar da ta gabata.

Ya ce an kashe malamin addinin ne a gonarsa da ke kusa da kauyen Rema, daga bisani aka dauki gawarsa aka kai asibitin Jibril Mai-Gwari da ke Birnin Gwari.

Ishaq ya ce an harbi malamin a cikinsa da kuma a kafadarsa.

Sai dai ya ce malamin ya riga mu gidan gaskiya wajen misalin ƙarfe 7:30 na yammacin Alhamis. Bugu da kari, sanarwar ta ce an kuma yi awon gaba da sama da mutum 40 a dajin Kuyambana, wanda bata-garin ke amfani da shi a matsayin maboya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: