‘Yan bindiga sun kashe wani Direba da yaron sa bayan sun bude musu wuta da bindiga kirar AK-47 akan hanyar Jiba-zuwa Batsari.
Lamarin ya faru ne a wani wuri da ake kira Sola dake karamar hukumar Jibia.
Shedun gani da ido sun ce lamarin ya faru ranar Talata ne bayan ‘Yan bindigar sun rufe hanyar shiga garin.
Kawo yanzu rundunar ‘Yan sandan Jihar basu tabbatar da faruwar lamarin ba.