‘Yan bindiga basu kai hari harabar Jami’ar Usman Danfodio ba – Isma’il Muhammad Yauri

0 290

Jami’ar Usman Danfodio da ke Sakkwato ta karyata labarin da ake yadawa cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a harabar jami’ar.

Jami’in hulda da jama’a na Jami’ar Isma’il Muhammad Yauri, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce babu wani hari da ‘yan bindiga suka kaiwa jami’ar.

Ya kuma bukaci jama’a da su yi watsi da rahoton, yana mai cewa labari ne marar tushe. Isma’il ya kara da cewa ‘yan bindiga sun kai harin ne kauyen Dundayen Bakin Gulbi don haka harin bai shafi al’ummar dake cikin jami’ar Usman Danfodio ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: