Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya yi kira ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya bi diddigin barayin man fetur, tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Da yake jawabi a wajen wani taron Cocin Godiya domin karrama babban sakataren kungiyar Evangelical Church a jihar Kaduna mai barin gado, Rabaran Yunusa Nmadu, tsohon kakakin ya ce kawo yanzu shugaban kasa Tinubu ya nuna jagoranci mai kyau kuma abun ya bawa ga dukkanin ‘yan kasa.
Ya kuma shawarci shugaban kasar da ya tabbatar da cewa an kwato dukkan kudaden da aka wawashe daga bangaren man fetir na kasar nan.
Dogara ya kuma yaba wa shugaban kasar kan nadin sabbin shugabannin tsaro da ya nada, inda ya ce Tinubu ya nuna jagoranci ta hanyar daukar kowane yanki ba tare da la’akari da jam’iyya, kabila ko addini ba.