Yakin Syria ya lakume rayukan yara dubu 22 cikin shekaru 10

0 187

Yayin da ake cika shekaru 10 da fara yakin kasar Syria, kungiyar dake sanya ido kan rikicin ta bayyana cewar ya zuwa yanzu yakin ya lakume rayukan mutane sama da dubu 388,000.

Kungiyar dake sanya ido kan rikicin kasar ta Syria tace daga cikin adadin mutane dubu 338 da 652 da aka kashe a cikin shekaru 10, sama da dubu 22 daga cikinsu yara ne kanana, kuma yawancinsu sun mutu ne sakamakon harin da sojojin gwamnati da ‘yan tawaye ke kaiwa.

Wani karamin. yaro mai suna Ahmed dake kukan rasa mahaifinsa Abdulaziz Abu Ahmed Khrer, wanda wani sojan Syria ya kashe.
Wani karamin. yaro mai suna Ahmed dake kukan rasa mahaifinsa Abdulaziz Abu Ahmed Khrer, wanda wani sojan Syria ya kashe. AP – Rodrigo Abd

Daraktan kungiyar Rami Abdel Rahman yace a shekarar da ta gabata ta 2020 kawai aka samu raguwar mace macen da ake gani a kasar, ganin cewar akalla mutane dubu 10 kawai suka mutu, saboda yarjejeniyar da bangarorin dake yakin suka kulla domin tinkarar annobar Korona.

Kungiyar dake sanya idon tace a cikin shekaru 10 da suka gabata, an samu mutane sama da dubu 16 da suka mutu a gidajen yarin gwamnati da wuraren da ake tsare da jama’a.

Yadda yaki ya ragargaza yankin Saif Al Dawla dake birnin Aleppo a kasar Syria.
Yadda yaki ya ragargaza yankin Saif Al Dawla dake birnin Aleppo a kasar Syria. AP – Manu Brabo

Daga cikin matsalolin da yakin ya haifar harda amfani da sinadari mai guba da ake zargin gwamnati da yan tawaye da kuma batar mutane akalla dubu 200 da ba’a san inda suka shiga ba.

Kungiyar tace duk da kwashe shekaru 10 ana gwabza wannan yaki, har yanzu gwamnatin Syria ke rike da sama da kasha 60 na yankunan kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: