Yajin Aikin Jami’o’i Na Daf Da Zuwa Karshe, Majalisa Zata Dauki Mataki

0 243

Majalisar Dattawa ta Najeriya ta kudiri aniyar daukan matakan gaggawa domin magance barazanar yajin aiki a jami’o’in kasar nan.

Yan majalisar sun yanke shawarar cewa shugabannin Majalisar su gana da Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i da kuma Kungiyar Ma’akatan da basa koyarwa.

Dukkan kungiyoyin 2, na barazanar tafiya yajin aiki domin neman kudade Naira Biliyan 30 na alawus-alawus da kuma nuna turjiya yadda Gwamnatin Tarayya taki bin umarnin kotu akan albashin malaman makarantun firemare da sakandire na cikin jami’o’i.

Kungiyoyin sun gudanar da zanga-zangar lumana ta kwanaki 3 da suka fara a reshen Jam’iar Ibadan domin neman bukatunsu.

Da yake kawo matsalar gaban Majalisa, Sanata Barau Jibrin,na jam’iyyar APC daga jihar Kano, ya shawarci abokan aikinsa da su lalabo hanyoyin magance yajin aikin.

Sanata Jibrin ya nuna cewa ana bukatar daukin Majalisar, duba da yadda har yanzu gwamnati mai ci bata nada ministoci ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: