Yadda ‘yan sanda suka cafke wata mata ‘yar shekara 20 bisa zargin ta da yunkurin kashe kanta

0 183

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Jigawa ta cafke wata mata ‘yar shekara 20 mai suna Dausiya Isyaku bisa zargin ta da yunkurin kashe kanta.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandar Jihar, Lawan Shiisu ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai jiya a Dutse.

Lawan Shiisu ya ce Dausiya Isyaku mazauniyar garin Roni a karamar hukumar Roni na jihar, ta aikata laifin ne a ranar 23 ga watan Yunin da ya gabata.

Lawan Shiisu ya ce ana cigaba da bincike a kan lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: