Yadda ‘yan bindiga sun sace ɗaliban firamare a Kaduna

0 336

Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da sace ɗaliban firamare da malamansu a ranar Litinin.

An sace ɗaliban ne a makarantar firamare ta Rema da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna, Samuel Aruwan, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa.

Wani jami’in gwamnati ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun kutsa kai cikin wani aji, inda suka yi awon gaba da yara biyu da malamansu biyu.

Wani mazaunin garin ya ce ya san malaman biyu da ake cewa an sace a makarantar.

Wani basaraken gargajiya da ya nemi a sakaya sunansa ya kara tabbatar wa da BBC faruwar lamarin a safiyar Litinin.

Wannan na zuwa ne a lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai hari wata makarantar sakandaren Ikara inda suka yi yunƙurin sace ɗaliban makarantar a daren Asabar.

Sai dai Samuel Aruwan wanda ya tabbatar da harin cikin wata sanarwa ya ce an daƙile harin ‘yan bindigar.

Ya ce,”an ceto dalibai 307 ba tare da sun samu wani rauni ba” a harin da sojoji suka murƙushe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: