’Yan bindiga sun mamaye Babban Asibitin Dansadau suna neman likitoci su je su kula da ’yan uwansu da aka ji wa rauni a cikin daji.
A mamayar ta Babban Asibitin da ke Karamar Hukumar Maru ta Jihar, maharan sun dauke ma’aikaciyar jinya da wata mai jinyar marar lafiya.
Mazauna garin sun ce bayan ’yan bindigar sun kai wani hari da misalin karfe 1 na dare ne suka kutsa kai tsaye zuwa sashen kula da marasa lafiya na asibitin suna neman likita ko nas-nas.
’Yan ta’addan dauke da makamai sun yi yunkurin kai hari ne a garin Maigoge, mai nisan kilomita shida arewa da garin Dansadau.
A halin da ake ciki, Shugaban Kungiyar Likitocin Najeriya, Reshen Jihar Zamfara, Dakta Mannir Bature wanda ya tabbatarwa manema labarai wannnan harin ya ce kungiyar ta damu da abin da ya faru, ya kara da cewa za su gudanar da taron gaggawa a jihar a yau Asabar domin tattaunawa a kan lamarin.