Yadda ‘wata mata ta kashe’ amaryarta mai kwana 54

0 287

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja a Najeriya ta tabbatar da kisan da wata mata ta yi wa kishiyarta mai suna Fatima wacce ba ta cika watanni biyu da auren ba ta hanyar duka da ƙona ta.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mohammed Adamu ya shaida wa BBC cewa sun samu labarin ne bayan da mijin matar mai suna Aliyu Abdullahi ya kai musu rahoto kan faruwar lamarin inda ya ce ya shiga gida ya taras an kashe amaryarsa.

Kuma in ji shi, binciken da suka gudanar ya nuna cewa an yi ta dukanta da taɓarya ko wai abu mai ƙarfi ne kafin a ƙona ta don nuna cewa ta mutu ne a sakamakon gobara.

Ya ce ”Akwai alamun cewa ita uwargidan da wata ƙawarta da ta taimaka mata sun yi mata dukan gaske da taɓarya ko kuma wani abu mai ƙarfi kafin su ƙona ta, don saboda duk da cewa ta ƙone akwai alamun duka a jikin gawar, mun kai gawar asibiti inda aka duba ta kafin mu miƙa wa danginta domin yi mata jana’iza.”

Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma kara da cewa yanzu haka uwaridan wato wacce ake zargi aikata kisan na hannunsu tare dsa sauran mutane uku da suka taimaka mata,

“Shekaran jiya mijin ya ce amaryar ta kawa fasfo din ta za a yi mata takardar izinin tafiya wato visa za su tafi umara ita da shi, wanda ya ce hakan ne me yiwuwa ya sa kishi ya motsa wa uwagidan ta yi wannan aika-aika,” in ji kwamishinan.

A nasa bangaren mahaifin marigayiyar, Malam Ibrahim Sidi na Khalifa da ke Sabuwar Unguwa jihar Katsina, ya shaida wa BBC cewa ya samu labarin rasuwar ‘yar tasa ne lokacin da ‘yar uwarta da ita ma ke aure a jihar Neja ta buga masa waya ta shaida masa abin da ya faru game da kisan Fatima.

“Jiya bayan Sallar Azahar mun gama cin abincin rana kenan, sai kawai yayarta Maryam ta bugo min waya cewa Baba sai dai hakuri kishiyar Fati ta kashe ta.

”Su biyu ne ‘ya’yana da ke aure a jihar Neja, kuma marigayiya Fatima duka-duka kwananta 54 da aure, sai kawai labarin mutuwarta na ji daga bakin ‘yar uwarta Maryam,” in ji shi.

Ya kara bayyana cewa: ”Da misalin karfe uku da rabi zuwa hudu na yamma, suka buga waya in bayar da izini a yi mata jana’iza, na ce ban yarda ba a kawo min ita gidana Katsina, an kuma kawo ta da misalin karfe hudu na dare,” in ji mahaifin marigayiyar.

Malam Ibrahim ya ce dama tun kafin nan da Fatima ta fahimci abin da ke shirin faruwa da ita ta y sauri ta kira ‘yar uwarta Maryam ta fada mata, inda ita kuma suka taho ita da abokiyar zamanta don su kai mata dauki, amma da suka iso sun riga sun hallaka ta.

Ya ce ”Bayanan da na samu, sai da matar ita da ‘yan uwan nata suka tabbatar babu kowa a gidan bayan da suka aiki masu gadi da ‘yan aikin gidan sai suka rufe kofofin gidan suka fara bugunta har sai da suka hallaka ta.”

Malam Ibrahim ya kuma kara shaida wa BBC cewa mijin marigayiya Fatima ya bugo masa waya da misalin karfe 12:20 na daren jiya inda yake tabbatar masa da cewa uwargidan tasa tare da ‘yan uwanta biyu suna hannun ‘yan sandan jihar Neja.

”Ya fada min cewa matar ta amsa cewa ta yi amfani da muciya tare da taimakon ‘yan uwanta biyu da suka rike ta suka yi ta dukanta,” in ji shi.

Amma ta buga wa ‘yar uwarta Maryam lokacin da ta ga alamun za su buge ta ta kira ‘yar uwur Maryam, sai ta taho ita da abokiyar zamanta suka tafi gidan amma lokacin da suka isa can har sun riga sun hallaka ta.

”Sai da suka ƙona wata riga suka dora a fuskarta suka ɓadda kamanninta, a takaice dai duk sun ƙona ta, wadanda suka duba ta sun ga babu komai da ya rage sai ƙashi kawai,”

Yawan kashe-kashen zafin kishi da ke jefa wasu mata musamman a arewacin Najeriya cikin halin aikata kisan kai ko na kishiya ko kuma mijin ya zama ruwan dare, inda a wasu lokutan ma matan kan kashe kansu da kansu saboda jin mijinsu zai kawo musu abokiyar zama.

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta ce ba a cika samun wadanda ke kashe mazajensu saboda kishi ba, amma sun taɓa samun wacce ta kashe kishiyarta a cikin shekarar da ta gabata a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: