Yadda wasu jirage suka halla shanu 1000 a Nassarawa.

0 229

Wasu jiragen saman yakin kasar nan sun hallaka sama da shanu 1000 a wani hari da suka kaddamar a matsugunni wasu Fulani dake Keana da karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa.

Wasu shuwagabannin Fulani da wadanda harin ya shafe su, sun gayawa manema labarai cewa an kaddamar da harin ne a ranar alhamis 10 ga watan Yunin nan da kuma lahadi 13 ga wannan watan.

Wasu shaidun gani da ido sun fadawa manema labarai cewa wasu matasan Fulani da dama sun samu raunuka daban daban, yayin da sama da shanaye 500 suka sangarta tare da tserewa zuwa jihar Benue dake makwabataka da jihar.

Haka zalika mazauna yankin sun bayyana cewa akalla shanaye 1000 ne aka kashe yayin harin a Giza dake karamar hukumar keana, a wani sumame da jami’ian tsaro suka kai garin domin fatattakar yan bindiga.

An gano cewa lamarin da ya faru a ranar lahadi an shafe sama da wanni 3 ana gudanar da shi,wanda ya sanya manoma da Fulani sukai ta tserewa zuwa domin tsira da rayuwar su.

Shugaban kungiyyar Fulani makiyya na jihar Bala Mohammed Dabo yace, an kai irin wannan harin a tsakanin Kwatanbala and Akwanaja dake Doma, wanda yayi sanadiyyar mutuwar shanaye 100.

Anasa bangaren mai magana da yawun hukumar sojin saman Nijeriya Edward Gabkwet ya gayawa manema labarai cewa ba jami’an su bane suka kaddamar da aikin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: