Yadda N50 Ta Yi Sanadiyyar Kisan Mutum 3 akan Caca

0 218

Akalla mutum uku ne aka kashe wani kuma na can kwance rai kwakwai mutu kwakwai a kan kudin caca N50.

Wakilinmu ya ga gano cewa wani mai suna Chidubem Mbamara ne ranar Juma’a ya shiga wani shagon caca na BetNaija dake reshen kasuwar Aba a Karamar Hukumar Ehime Mbano a jihar Abiya da nufin yin cacar.

Rahotanni sun ce Mista Chidubem ya shiga cacar da ta kai N600 duk da yake ba shi da isassun kudin da zai biya a hannunsa.

Hakan ne ya sa ya biya N150 sannan ya bayar da jinginar wayarsa da nufin ya je gida domin dauko cikason kudin.

To sai dai bayan dawowarsa sai ya biya N400, jimlar N550 kenan, sannan ya yi alkawarin ciko N50 kashegari.

Daga nan ne kuma lamarin ya janyo cece-kuce da muhawara mai zafi tsakaninsa da manajan shagon mai suna Mista Henry Obi.

Rahotanni sun ce hassala Chidubem da aka yi ne ya sa ya koma gida sannan bayan wasu ’yan mintuna ya dawo da karamar bindigar Pistol kirar gida, nan take kuma ya harbe Henry Obi inda harsashin ya kuma sami wani mai suna Chibuike Iwunze da kuma wani Ebuka.

Hakan ne ya sa wasu mutane suka fusata inda suka far wa Mista Chidubem da duka har sai da shima ya ce ga garinku nan.

Henry dai da Ebuka nan take suka mutu, yayin da shi kuma Iwunze na can kwance ranga-ranga yana fama da rashin lafiya a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar, Orlando Ikeokwu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Nasiru Mohammed ya fadada bincike a kan lamarin, yayin da aka kai gawarwakin wadanda suka mutu dakin adana gawarwaki.

Ya shawarci jama’a da su kaucewa daukar doka a hannunsu sannan su rika kai rahoton duk wata rashin jituwa domin daukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: