Yadda Kidan Gangin Tsadar Rayuwa Ke Kara Firgita ’Yan Najeriya

0 180

Abubuwa da dama ne su ka haddasa kayan abinci yin tsadar da tsawon shekaru 15 baya ba su kamar haka ba.

Akwai dalilai na matsalar tsaro, sai barkewar cutar korona, sai canjin yanayi da sauye-sauyen tsarin tafiyar da tattallin arziki, duk wadannan sun cilla farashin kayan abinci sama, fiye da karfin aljihun milyoyin ’yan Najeriya.

Shekaru 15 rabon da a yi kuka da farashin kwan kaji kamar wannan shekarar, kamar yadda masu sayen kwan kaji su ci da masu sayar da shi su ka bayyana wa PREMIUM TIMES.

A cikin watan Fabrairu, 2021 dai sai da farashin kayan abinci ya karu da kashi 27 bisa kashi 100, kamar yadda Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS) ta bayyana.

Yadda Kidan Gangin Tsadar Rayuwa Na Kara Firgita ’Yan Najeriya:

Farashin ya nuna ya hauhawar da tun cikin 2005 ba a yi kuka da wannan tsadar ba kamar bana.

*Buhun shinkafar da ake sayarwa naira 7,000 cikin 2016, a yanzu naira 40,000 ake sayar da irin sa.

. Ledar markadadden tumatir wadda a baya-bayan nan aka rika sayarwa naira 50, a yanzu ta cilla sama zuwa naira 250 wasu wuraren har naira 400. Ko ka saya ko ka ci tuwo gaya ba miya.

A yanzu talaka kallon-tsoro ya ke wa kazar Hausa ballantana ta gidan-gona. Kaza mai nauyin kilo daya da ake sayarwa naira 800 a baya, yanzu ta kilo daya ya kai naira 2,000.

Yayin da talaka ke gaganiyar yadda zai yi miya da daddawa, farashin kwan kaji yanzu kires daya ya kai naira 1,500.

Yayin da PREMIUM TIMES ta binciko dadilai da dama wadanda su ka haddasa tsadar kayan abinci, har yanzu duk da makudan kudaden da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke narkawa a harkar noma, babu wata alamar da ke nuna cea an kamo hanyar magance tsadar kayan abincin.

Tattaunawar da aka yi masu kiwon kaji, masu sassafa abincin dabbobi da na kaji sun bayyana tsadar waken soya da tsadar masara na daga cikin abinda ya haddasa tsadar abincin kaji, wadda ita din ce ta haddasa tsadar kaji da tsadar kwan kaji, ta yadda talaka sai dai ya gani a kasuwa, ya wuce ko tayawa ba ya iya yi.

Ga kuma gagarimar matsalar tsaron da ke hana noma a wasu yankuna, hana cin kasuwanni da kuma sace amfanin gonar da manoma su ka noma ko lalata masu kayan gonar tun kafin su girbe.

“Ka ga fa tan daya a yanzu da a da ake sayarwa naira 108,000 zuwa naira 110,000, yanzu ya kai naira 500,000” Inji wani mai suna Awwal.

“Kuma ka ga shekara daya da ta gabata, abincin kaji ana sayar da buhu daya naira 2,900. Yanzu kuwa ya kai naira 6,500.

Yadda Masara Ke Zazzare Wa Talakawan Najeriya Idanu:

Shugaban Masu Kiwon Kaji na Najeriya, Reshen Jihar Kaduna, ya bayyana cewa a shekarar 2020 naira 90,000 ake sayar da tan daya na masara. A yanzu kuwa tan daya ya kai naira 195,000.

Timothy Okunade ya kara shaida wa PREMIUM TIMES cewa waken soya yanzu ya kai naira 310,000 tan daya, a shekarar 2020 kuwa naira 130,000 ya ke.

Okunade ya kara da cewa noma yanzu ya zama abin tsoro. Manomi na gudun fita gona masu garkuwa su damke shi, sai ya sayar da gonakin sa ko ma har da gidajen kafin ya fanshi kan sa.

Wannan dalili da kuwa wasu dalilai sun haifar da tsadar kayan abinci. Wasu kuma sun a saye sun a kimshewa, tsoron kada kayan abincin ya yimatukar karanci nan gaba kadan kafin zuwan wata kayar dibar amfanin gona.

Dangane da matsalar tsoro, a jihar Kaduna kadai, an kashe mutum 937 cikin 2020. Sannan kuma a dai cikin wannan shekarar ta 2020, an yi garkuwa da mutm 1,972 a jihar Kaduna, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana a cikin wannan wata na Maris.

Tun Da Mu Ka Kori PDP Buhun Shinkafa Ya Gagare Ni:

A Kano, wani ladani da ya nemi a sakaya sunan sa, ya bayyana wa wakilin mu cewa a gaskiya rayuwa ta yi masa tsanani a yanzu.

“Mu da kan mu mu ka rika addu’a Allah ya raba mu da gwamnatin da ta gabata. Mu ka ce canji mu ke so. To amma ina tabbatar maka ni dai tun da wannan gwamnati da na dangwala wa kuri’a daga sama har kasa ta hau mulki cikin 2015, har yau wallahi ban iya sayen buhun shinkafa, kamar yadda na ke iya saye a zamanin gwamnatin da muka kora ba.”

Malamin wanda ke zaune a Dandinshe, amma ya na ladanci a can wata unguwa, ya ce a yanzu sai dai ya auni mudun shinkafa kawai ya kai gida, idan ta kare kuma ya rika gaganiyar yadda zai sake sayen wata, tunda albashin sa bai taka kara ya karya ba.

An Shafe Kwanaki 20 Ba A Yi Miya Da Nama Ko Kifi A Gida Na Ba:

Haka shi wa wani tsohon jami’in tsaron da ya yi ritaya, ya shaida wa wakilin mu cewa a baya mutum ya yi kadan ya tsaya a gaban sa ya na sukar wannan gwamnatin. Amma ya ce lamarin ya firgita shi yayin da ya shafe kwanaki 20 ba a yi miya da nama ko kifi a gidan sa ba.

“Ni gaskiya zan fada cewa kuri’ar da na damgwala, ashe dangwalo wa kai na fatara na yi. Amma ba na son ka buga suna na, don kada ’yan adawa su rika yi min dariya.” Inji shi, a tattaunawar da da wakilin mu wani yammaci a kofar gidan sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: