Kungiyar Chelsea a gasar Premier League ta Ingila, ta zubar da damar da ta samu ta taka rawar gani a gasar, bayan da suka tashi canjaras da Leeds.
Sai dai wannan sakamako na nufin, har yanzu Chelsea ba ta sha kaye ba karkashin jagorancin sabon kocinta Tuchel.
Duk da da cewa bangarorin biyu wadanda suka kara a ranar Asabar, ba su da magoya bayan da za su kara musu kaimi a filin wasan, dukkansu sun nuna bajinta a wasan.
Sai dai sabanin wannan wasa, Manchester City ta lallasa Fulham da ci 3-0 lamarin da ya kara mata damar zama daram a saman teburin gasar ta Premier.
Wannan sakamako na nufin City ta ba da tazarar maki 17, yayin da Manchester United wacce ke da wasanni biyu da za ta buga a nan gaba take biye da ita.
Yanzu City na da maki 71, United na da maki 54, Leicester na da maki 53 a matsayi na uku a teburin gasar ta Premier.
A wasannin kuma da za a buga a ranar Lahadi, Southhampton za ta kara da Brighton, Leicester za ta gwada kaiminta da Sheff United, yayin da Arsenal za ta karbi bakuncin Tottenham.