Yadda Ake Warware Sihiri Cikin Sauƙi Daga Sheikh Dr. Isah Ali Pantami

0 3,502

1. A samu ruwa mai tsafta, gayen magariya koraye masu kyau guda bakwai (idan an samu busassu sunfi), sai a niqa a zuba cikin ruwan.

2. Sai a karanta suratul fatiha a cikin sa, kuma a dinga yi nunfashi yana shiga cikin ruwan.

3. Sai a karanta Ayatul Kursiyyu (aya ta 255 na cikin suratul Baqara).

4. Sai a karanta Suratul A’araf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122.

5. Sai a karanta Suratul Yunus daga kan aya ta 79 zuwa kan aya ta 82.

6. Suratul Kafirun kafa daya

7. Falaki da Nasi kafa uku- uku.

8. Sai a karantan wannan addu’a “Allahumma rabban-nas az’hibil ba’as ashfi wa antash-shafi la shifa’a illa shifa’uk shifa’un la yugadiru saqaman” kafa uku.

Sheikh Dr. Isah Ali Pantami

9. Sannan za’a iya karawa da wannan addu’a “Bismillahi urqiqa min kulli shai’in yu’uziyka wa min shairi kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urqiqa” kafa uku

10. Insha Allahu ta’ala idan aka karanta wadannan, kuma mutum ya dinga sha so biyu a rana safiya da yamma, ya kuma dinga wanka dashi a waje mai tsarki, ko kuma ya samu tawul ya jika da ruwan ya dinga gogawa a jikin sa, Insha Allah nan da sati guda kowani irin sihiri ne Allah (S.W.T) zai karya shi.

Basai mutum yaje wajen boka an danfare shi ba. Kamar yadda Malam yake fadi basai an maka/ miki sihiri ba, mutum zai iya yi domin tsima jikin sa daga shairin mashairranta.

Don karin bayanin za’a iya neman Fat-hul Majid shair’in Katibu Tauhid babin “Annushra” > Fatawa na Bin Bass juzuhi na 8 shafi na 188 yayi dogon bayani akai. > Sannan littafin “Assarimul Battar fi tasaddi li saharatul ashrar” na Dr Wahid Abdus-salam Bali.Allah yasa mudace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: