Wani kusa kuma jagora a yankin Neja Delta Chief Edwin Clark ya ce ya zama dole wanda zai shugabanci kasar nan a shekarar 2023 ya kasance ya fito ne daga yankin kudu maso gabashin kasar nan.
Jagoran ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa Senata Anyim Pius Anyim jiya a Abuja.
A cewar sanarwar da aka fitar bayan ziyarar ance Clark ya bukaci Anyim da yayi aiki tukuru da sauran shugabanni a fadin kasar nan domin samar da matsayar rabadai-dai da tsagin kudu maso gabashin kasar nan, tsagin dake zargin anyi shakulatin bangaro dasu wajen rike madafun iko.
Kazalika Clark ya jaddada bukatar lallai-lallai dan takarar shugabancin kasar sai ya kasance daga kudancin kasar nan musamman yankin gabas.
Da yake martani dangane da batun Anyim yace da Chief Clark wanda tsohon ministan ma’aikatar yada labarai ne a jamhuriya ta farko, ya ce yana neman takarar shugaban cin kasar nan musamman ganin yadda lamura suka dagule.
Anyim wanda shima tsohon shugaban majalisar dattawa ne yana neman tikitin tsayawa takarar ne karkashin tutar jamiyyar PDP.