“Ya kamata a soke kundin tsarin mulkin Nijeriya” – Babban Lauya, Prof Sagay

0 191

Wani babban lauya a Nijeriya Farfesa Itse Sagay, ya yi kiran da a soke kundin tsarin mulkin Nijeriya.

A cewarsa, kundin tsarin mulkin jamhuriya ta farko na shekarar 1963, ya magance duk wasu batutuwa da ake hankoro a kan su don magance matsalolin da kasar ke fama da su.

Sagay, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin ba shugaban kasa shawara kan yaki da cin hanci, ya yi bayanin cewa, kamata ya yi a waiwayi rahoton kwamitin da jam’iyyar APC ta kafa kan sauya fasalin Nijeriya, wanda Nasir El-Rufa’i ya jagoranta.

Ya ce rahoton kwamitin ya zo da kyawawan shawarwari da ya kamata a duba tare da aiwatar da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: