Woodberry Abokin Aikin Hushpuppi Ya Amsa Laifin Zamba Da Ake Tuhumarsa A Kotun Amurka

0 150

Olalekan Jacob Ponle, sanannen mai hannu da shuni ne kuma aminin dan damfaran intanet na Najeriya, Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi, ya amsa laifin zamba da aka yi masa a wata kotu a Amurka.

Wanda aka fi sani da Mista Woodberry, ya amince ya yi asarar dalar Amurka miliyan 8 daga cikin kudaden da aka samu daga tsarin zamba ta Internet.

 An tattaro cewa wani bangare na cinikin nasa ya hada da kwace motocinsa na alfarma, agoguna da kayan sawa masu tsada da gwamnatin Amurka ta kwace.

Yayin da motocin alatu Woodbery zai rasa sun hada da, Rolls Royce Cullinan, Lamborghini Urus (N4973) da Mercedes-Benz G-class. An kuma bukaci ya yafe masa hakkinsa na motocin alfarma, da agogon zanen da ya ajiye a Dubai.

A cikin yarjejeniyar da ya shigar, an bukaci ya biya dala miliyan 8 da ya karba a zamba daga kamfanoni bakwai da ya zamba ta. Woodberry kamar abokinsa Hushpuppi, kafin a kama shi, an san shi da nuna kyakykyawar salon rayuwarsu a shafukan sada zumunta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: