William Ruto ya sanar da korar ministocinsa sakamakon boren da gwamnatinsa ta fuskanta

0 174

Shugaban Kenya William Ruto, ya sanar da korar kusan dukkan ministocinsa sakamakon boren da gwamnatinsa ta fuskanta daga jama’a saboda tsadar rayuwa.

A jawabin da ya yiwa al’ummar ƙasar ta kafar talabijin, Ruto yace waɗanda korar bata shafa ba sune mataimakin shugaban ƙasa Rigathi Gachagua da kuma ministan harkokin waje Musalia Mudavadi.

Al’ummar Kenya dai, sun ƙalubalanci gwamnatin ƙasar da rashin iya jagoranci, inda suka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da kuma ta adawa da sabon harajin da gwamnati ta yi shirin ɗora musu, har ta kai ga rasa rayuka.

Ana ta raɗe-raɗin cewa shugaban na shirin kafa wata sabuwar ƙaramar gwamnati ne sakamakon zanga-zangar da aka kwashe makonni ana yi.

Shi dai, Ruto ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan ya saurari jama’a, kuma nan take zai shiga tattaunawa mai zurfi a mabanbantan ɓangarori da jam’iyyun siyasa da sauran al’ummar ƙasar ta Kenya, domin kafa gwamnatin da za ta wakilci kowa da kowa.

Ya ƙara da cewa hakan ya zama wajibi ne domin haɗa ƙarfi da ƙarfe wurin kai wa ƙasar ga tudun mun tsira, sakamakon katutun matsalolin tattalin arziki da walwalar jama’a da suka dabaibayeta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: