Wata gobara ta kone wani sashe na shahararriyar kasuwar Gujungu a yankin Karamar Hukumar Taura a jihar Jigawa.
Kakakin hukumar civil defense na jiha, Adamu Shehu, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.
Yace gobarar ta fara daga kantinan sayar da tufafi da misalin karfe 4 na yammacin Talata.
Adamu Shehu yayi bayanin cewa gobarar ta lalata kimanin kantina 250 tare da kayayaki na miliyoyin nairori.
Yace har yanzu ba a san abinda ya haifar da gobarar ba.
A wani labarin kuma, babban sakataren hukumar agajin gaggawa ta jiha, Alhaji Yusuf Sani Babura, yace gwamnatin jiha tana kokarin tallafawa wadanda lamarin ya shafa.
Ya danganta aukuwar gobara kan yawaitar amfani da wuta da wasu ‘yan kasuwa suke yi domin dumama jikinsu, ko gasa kifi ko nama, ko wani abu makamanci.
Shugaban kasuwar, Alhaji Salisu Dan’azumi, shima ya tabbatar da aukuwar lamarin ga wakilinmu, inda yace gobarar ta lashe kayayyaki na sama da naira miliyan 10.