Gwamnatin Tarayya tace zata kafa wani kwamiti cikin mako mai zuwa domin sake fasalin yadda ake rabon arzikin kasa tsakanin gwamnatin tarayya, jihoshi da Kananan Hukumomi.
Shugaban Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Kasa, Mista Elias Mbam, shine ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, jim kadan bayan ya karbi kyautar girma daga kungiyar ma’aikatan gwamnati a Najeriya.
A yadda rabon arzikin kasa a halin yanzu, gwamnatin tarayya ke daukar kaso 52.68 cikin 100, jishoshi kuma su raba kasha 26.72 cikin 100, yayinda kananan hukumomi suke raba kasha 20.6 cikin 100.
Haka kuma, ana ware kasha 13 cikin 100 na kudaden da aka samu daga man fetur da iskar gas, inda ake mikawa jihoshin da ake hako mai daga yankinsu, domin mayar musu da asarar gurbatar yanayi da hako man ke jawowa.
An ratsa hakan ne zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
Kazalika, hukumar taga bukatar sake bibiyar yadda ake rabon a shekarar 2013, domin tabbatar da adalchi da daidaito wajen cigaban kasa, kuma sai ta fara yawon tuntuba tare da tattaunawa da manyan mutane akan maganar.
A watan Dismanbar 2014, hukumar ta fitar da sabon tsarin rabon, amma saboda wasu dalilai, ba a fara aiki da shi ba.
Shekaru 5 baya, shugaban hukumar yace hukumar tana shirin kafa kwamiti sati mai zuwa domin sake bibiyar tsarin rabon.