Wata Mata Ta Kashe Mijinta Har Lahira Akan Cajar Waya A Katsina

0 313

Wata matar aure yar shekara 17 mai suna Rabi Rabiu, ta kashe mijinta har lahira mai suna Shamsu Salisu a ranar Larabar da ta gabata a jihar Katsina, a lokacin da suke jayayya da juna wajen sa cajin wayoyin salula wanda ya kai ga rashin jituwa tsakanin ma’auratan.

Rabi wacce yanzu ke tsare a hannun yan sandan jihar Katsina ranar Talata tace bata yi tsammanin wukar da ta sokawa maigidan nata Salisu mai shekara 25 zata kai ga rasuwarsa ba.

Kamar yadda tace al’amarin ya faru ne a safiyar ranar Laraba lokacin da aka kawo wutar lantarki, tana kokarin sa cajin wayarta ta hannu, shi ma mijin nata yana kokarin sa ta sa wayar, hakan ya kai ga rashin jituwa tsakanin ma’auratan.

Salisu ne yayi yunkurin daukar wuka da farko, cikin zafin hunnu Rabi ta kwace wukar daga hannunsa, a cewarta.

Cajar Waya

Rabi tace kwanansu 51 da angoncewa, suna san junansu ba tayi tsammanin saran zai kai ga mutuwarsa ba.

mai Magana da yawun hukumar yansanda, SP Gambo Isah a shalkwatar yansanda ta malumfashi ,ya bayyana mutuwar matashin wanda mai dakinsa Rabi Rabiu yar shekara 17  ta hallaka, lokacin da yake bacci, rabi ta soke shi da wuka a sassa daban na jikinsa harda cikinsa.

Ya samu manyan raunuka a jikinsa, wanda yansanda suka garzaya dashi babbar asibitin Malumfashi sannan aka tabbatar da mutuwarsa.

Yansanda sun sami wuka, da mayafi wanda ke jike da jini lokacin da suka je inda abin ya faru.

Leave a Reply

%d bloggers like this: