Wata kungiyar bayar da agaji ta ActionAid ta tabbatar da shirin ta na kawo karshen matsalar yara da basa zuwa makaranta a jihar Yobe, wanda daya ne daga cikin manufofin kungiyar.
Daraktar shirye-shirye ta kungiyar a Najeriya Hajiya Suwaiba Ibrahim, ta bayyana haka yayin da take mika aikin gyaran ginin makarantar firamare dake Tarabutu a karamar hakumar Murtsari a jihar Yobe.
A cewarta hakumar kididdiga ta kasa ta ce sama da yara dubu 427, 230 basa zuwa makaranta a jihar yobe, kuma alkaluman sun bayyana kaso 43 na yawan yaran da ake dasu a jihar baki daya.
Kungiyar zata tallafa wajen ciyar da ilimi a matakin farko a jihar ta Yobe domin rage matsalar.
- Comments
- Facebook Comments