Wata kungiya mai zaman kanta ta tallafawa mata marasa galihu guda 100 da kudi dan rage radadin talauci

0 280

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Dangin Juna Africa Initiative ta tallafawa mata marasa galihu guda 100 da naira dubu biyar kowannensu, domin rage radadin matsalar tattalin arziki.

An bai wa matan kudin ne a yayin bikin murnar cikar kungiyar shekaru 6 da aka yi a garin Deba na karamar hukumar Yamaltu/Deba ta jihar.

Shugaban kungiyar, Bashir Sani Dogo, ya ce hakan daga yanzu zai zama wani bangare na ayyukan kungiyar, wanda za a bai wa masu karamin karfi da marasa galihu jari duk shekara yayin bikin zagayowar cikar shekarun kafa kungiyar.

Shugaban Karamar Hukumar Yamaltu/Deba, Shu’aibu Umar Galadima, ya yabawa kungiyar kan kokarin da ta yi.

A jawabinsa, Mai Martaba Sarkin Deba, Alhaji Ahmed Usman, ya jinjina wa kungiyar bisa wannan karamci, yana mai cewa shiri ne mai kyau mutane su rungumi juna da taimakon mabukata domin rage talauci da zaman kashe wando.

Leave a Reply

%d bloggers like this: