Wata guguwa ta halaka mutane aƙalla 50 bayan da tai muguwar tasowa a gabashin Amurka

0 355

Wata guguwa ta halaka mutane akalla 50 bayan da ta afkawa Kentucky da ke kudu maso gabashin Amurka, kamar yadda gwamnan jihar Andy Beshear ya shaida wa manema labarai.

Gwamnan ya kuma bayyana fargaba kan yiwuwar adadin mamatan ya zarce zuwa 70 ko 100 la’akari da cewar kakkarfar guguwar ce mafi hatsari a tarihi da ta afkawa jihar tasa.

Guguwar dai ta lalata larduna da dama a jihar ta Kentucky, yayin da take tsala gudun kilomita kusan 240 cikin sa’a guda.

Tuni dai guguwar ta yi barna a wasu sassan jihohin Amurka baya ga Kentucky, inda a ranar Juma’a ta yi kaca kaca da wani babban shagon sayar da kayayyaki na Amazon da ke jihar Illinois, yayin da kafafen yada labarai na cikin gida suka ba da rahoton cewa akwai kusan ma’aikata 100 makale a cikin sauran ginin katafaren shagon.

Jami’ai dai na cigaba da aikin ceto wadanda guguwar ta rutsa da su.

A jihar Tennessee kuwa, akalla mutane biyu ne suka mutu sakamakon guguwar da ta afku, kamar yadda wani jami’in bayar da agajin gaggawa ya shaidawa kafafen yada labaran cikin gidan Amurka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: