Wani shagalin bikin daurin aure ya rikide zuwa makoki bayan da aka yi zargin wata amarya ta sanya guba abincin bikin liyafar ta.
Lamarin dai ya rutsa da angonta wanda ke kwance a asibiti, sai kuma wani mutum guda da ya rasa ransa sanadin cin abincin mai dauke da guba.
Lamarin dai ya faru ne a karamar hukumar Jahun da ke nan jihar Jigawa.
Shaidun gani da ido sun gayawa manema labarai cewa mai yiwuwa ne wani ne ya zuga amaryar ta aikata wannan danyen aiki a ranar bikin ta.
Da yake zantawa da manema labarai, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce suna gudanar da bincike.
yace wadanda ake zargin su biyun amarya ne da wata kawarta, wanda yanzu haka suna tsare a hannun hakuma ana yi musu tambayoyi a sashin binciken manyan laifuka na rundunar.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, an sallami dukkan mahalarta bikin auren da suka ci abincin mai dauke da guba daga asibiti, sai dai mutum guda da aka tabbatar ya mutu.
Kawo yanzu dai Hukumomi ba su bayyana sunayen wadanda suka mutu, angon, da sauran wadanda abin ya shafa ba.