Ƙungiyar CISLAC mai sanya idanu kan ayyukan majalisa a Najeriya ta yi tur da matakin Babban Bankin ƙasar, CBN na zargin facaka da kuɗaɗe masu yawa kan shugabaninsa, lokacin da ake fama da matsalar yunwa da hauhawar farashin kayayyaki.
Cikin wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun babban daraktanta Auwal Musa Rafsanjani, ƙungiyar ta ce an kashe kuɗaɗen ne kan shugaban bankin Yemi Cardoso da wasu mataimakansa huɗu.
CISLAC ta yi iƙirarin cewa Cardoso da mataimakansa da Majalisar Dattijai ta amince da naɗinsu a watan Satumbar 2023, sun kashe wa kansu naira biliyan 10 wajen sayan motoci masu sulke.
Daga bayanan da CISLAC ta samu ta ce “Mista Cardoso ya bayyana cewa ya saya wa kansa da mataimakansa motoci ƙirar Lexus LX 600 2023. Mataimakan nasa sun haɗa da Emem Usoro da Philip Ikeazor da Bala Bello da kuma Sani Abdullahi.
Majiyar CISLAC daga CBN ta shaida cewa Cardoso ya saya wa kansa wasu motoci biyu ƙirar SUV da zai riƙa amfani da su a Legas da Abuja duk da cewa akwai motoci masu sulke a tawagarsa da yake tafiya da su kusan koda yaushe.
Ƙungiyar ta kuma yi zargin Mista Cardoso ya sayi motoci ƙirar Toyota Camry sabbi guda 20 kan kuɗi naira miliyan 85 kowacce ɗaya, ya kuma raba su ga mambobin kwamitin amintattu na CBN.
Wani rahoton da CISLAC ta samu daga cikin CBN ya ce gwamnan bankin da mataimakansa sun ƙara wa kansu kudin alawus na gida zuwa kusan naira biliyan ɗaya a shekara ɗaya, duk da cewa suna zaune ne a gidajen gwamnati na alfarma da ke Maitama a Abuja.