Wasu yan bindiga sun sace wani Kanal mai ritaya da yayan sa 2 a hanyar Gusau-Tsafe da ke jihar Zamfara

0 240

Wasu yan Bindiga sun sace wani Kanal Mai Ritaya mai suna Rabiu Yandoto da yayan sa 2 a hanyar Gusau-Tsafe da ke Jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin Mohammed Hassan, shine ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce yan bindigar sun sace Yandoto tare da yayan sa biyu inda suka shiga da su cikin Daji a lokacin da ya ke kokarin tafiya gida jiya da daddare.

Kanal Rabiu Yandoto mai ritaya, ya yi kaurin suna wajen sukan Sanata Kabitu Marafa, a zaben da ke tafe na shekarar 2023.

Mutumin Jagora ne a Jam’iyar APC kuma shine ya kafa Kungiyar ‘‘APC Wake da Shinkafa’’ domin tabbatar da cewa Sanata Marafa mai samu nasara a kujerar Sanata ba a zaben 2023 mai zuwa.

An yi kokarin tuntubar Kakakin Rundunar yan sandan Jihar Zamfara SP Muhammad Shehu, amma abin ya ci tura.

Leave a Reply

%d bloggers like this: