Wasu Ne Ke Son Bata Min Suna Da Shafukan Sada Zumunta – Nmadi Sambo

0 201

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Namadi Sambo ya bayyana amfani da sunansa da ake yi a kafar sada zumunta ta Facebook da sauran hanyoyin sadarwa na zamani da cewa wadansu bata gari ne cikin al’umma ke amfani da sunansa ta wadannan hanyoyi.

Namadi ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da sanyawa hannu ya kuma rabawa manema labarai a garin Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar, anyi amfani da dandalin na sada zumunta inda aka rubuta cewa yana goyan bayan batun juyin juyin halin da Injiniya Mista Omoyele Soware ya jagoranta wanda yanzu haka yake hannun jami’an tsaro na farin kaya suna gudanar da bincike akansa.

Sakon wanda aka wallafa a shafin sada zumunta na facebook ana zarginsa da cewa mallakar Namadi Sambo ne kuma shi ke tafiyar da harkokinsa a shafin.

Haka nan sakonnin da aka wallafa a shafin sun yi zargin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsare tsohon mai bawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathon da kuma shugaban kungiyar yan uwa Musulmai ta Shi’a Sheik Ibrahim Zakzaky tare da matarsa Hajiya Zeenat ba tare da dalili ba.

Kazalika tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu tantance labaran kanzon kurege dake yawo ta hanyoyin sada zumunta da kuma duk wata Magana marar tushe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: