Wasu mata hudu sun mutu a wani mummunan hatsarin mota a karamar hukumar Malam Madori
Wasu mata hudu sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a hanyar Garun Gabas da ke karamar hukumar Malam Madori.
Dukkan mamatan, shekarunsu ba su wuce 30 ba, kuma suna kan hanyarsu ne ta komawa gida lokacin da motar hayar ta daki wani rami akan titin kuma ta auka cikin wani tafkin dake kusa. An yi jana’izar mamatan, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a garinsu na Ciromari.
Shugaban karamar hukumar Mallam Madori Hussain Umar BK ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa tare da yin addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba su hakurin jure rashin.