Wasu maharan kwanton-bauna sun bude wa jami’an ‘yan sanda da fararen hula wuta a Fatakwal

0 220

Yankin Kudu-maso-Kudu ya kamo hanyar gwadaben da Yankin Kudu-maso-Gabas ya dauka, inda mazauna jihohin su ka fara yin bankwana da zaman lafiya.

Wasu maharan kwanton-bauna sun bude wa jami’an ‘yan sanda da fararen hula wuta a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

Wannan wani mummunan lamari ne ga jami’an tsaro, ganin yadda ake bin su daya bayan daya, ana kai masu hare-hare da kisa a ofisoshin su da kuma kan manya da kananan titinan kudancin kasar nan.

Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Ribas, Nnamdi Omoni ya tabbatar da cewa sun samu labarin kisan da wasu da ba a kai ga gano su ba, su ka yi wa jami’an tsaron su.

Ya ce zuwa yanzu ba a kai ga tantance wadanda aka kashe din ba tukunna. Amma Kwamishinan ‘Yan Sandan Imo ya kafa kwamitin binciko lamarin tare da shan alwashin kamo wadanda su ka yi wannan aika-aika.

Sai dai kuma wasu mazauna Fatakwal sun ce da idanun su sun ga gawarwakin mutum takwas, wadanda biyu daga cikin su gawarwakin ‘yan sanda ne.

Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya bayyana wadanda su ka yi kisan cewa “babbobi ne, kuma sun aikata dabbanci.”

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labaran sa Kelvin Ebiri ya fitar, ya bayyana cewa Gwamna Wike ya bayyana goyon bayan sa ga dukkan tsaron da jami’an tsaro ke dauka, domin dakile matsalar tsaro a jihar Ribas.

Ya nemi jami’an tsaro su kara mikewa tsaye wajen kare kan su da kare al’umma baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: