Wasu fusaattun matasa sun kone wasu gidaje 24 tare da rumbunan abinci 16 a jihar Jigawa

0 57

Anyi zargin wasu fusaattun matasa daga Zangon Maje sun kone wasu gidaje 24 tare da rumbunan abinci 16 a kauyen Gidan ruwa dake karamar hakumar Taura a nan jihar jigawa.

Wani mazaunin kauyen gidan ruwa ya sanar da manema labarai cewa lamarin ya faru ne a jiya litinin, lokacin da wasu gungun mutane dauke da makamai suka kai hari kauyen.

Yayi bayanin cewa, lokacin da suka hangi jama’ar masu yawa daga dayan bangaren dauke da fitulu a cikin dare suna rera wakokin yaki, mutanen garin suka fara barin gidajensu domin tsira da raywur su.

Kakakin yansandan jihar Jigawa SP. Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da aukuwar lamarin gay an jarida.

Yace lokacin da suka samu rahoton faruwar lamarin, sun tura jami’an sintirinsu zuwa wajen da abin ya faru.

Shiisu Adam yace bincikin yansanda na farko ya gano cewa, tashin hankalin ya samo asali ne lokacin da aka daki wani matashi Musa Hussaini da abokinsa Shanu Sule da sanda tare da kwace musu babur ne, suka sanar da jama’ar kauyen su domin daukar fansa.

Amma Shiisu Adam yace hankula sun koma daidai yayin da aka aike da jami’an yan sanda yankin.

Haka kuma kakakin yan sandan yace sun kama mutane 5 bisa zargi da hannu a tashin hankalin domin gudanar da bincike.

Leave a Reply