Wasu fitattun mutanen yankin arewa sun kaddamar da wani dandamali kan dabarun magance matsalolin tattalin arziki da tsaro a yankin
Wasu fitattun mutane maza da mata na yankin arewa sun kaddamar da wani dandamali mai zaman kansa kan dabarun magance matsalolin tattalin arziki da tsaro a yankin.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya ruwaito cewa wasu daga cikin mutanen da suka hada jadawalin taron sun hada da dattijo Alhaji Bashir Tofa da tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega, da sauran su.
Da yake yiwa manema labarai karin haske, a jiya, a Abuja, Bashir Tofa, tsohon dan takarar Shugaban kasa na tsohuwar Jam’iyyar NRC, ya yi bayanin cewa an kafa kungiyar ne a matsayin dandamali don magance matsalolin rashin tsaro da rashin ci gaba a yankin.
Tofa ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki, musamman na siyasa, kasuwanci, fasaha, gargajiya, addini, al’umma da shugabannin matasa da su tallafa wa shirin domin sake fasalin yankin arewa gaba daya.