Wani Minista ya bukaci hukumomin dake yaki da rashawa da su kama Gwamna Samuel Ortom

0 152

Ministan ayyuka na musamman, Sanata George Akume, ya bukaci hukumomin dake yaki da rashawa da su kama Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue.

George Akume, wanda tsohon gwamnan jihar Benue ne, yayi kiran a yau, a wajen taron manema labarai a Abuja.

Tsohon gwamnan ya kuma bukaci Gwamna Samuel Ortom ya daina sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Taron manema labaran ya samu halartar dattawa da masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC a jihar Benue.

Gwamna Samuel Ortom na fama da fadi tashi tsakaninsa da fadar shugaban kasa dangane da rikicin manoma da makiyaya da kuma rashin tsaro a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: