Wani magoyin bayan Abba Kabir Yusuf ya rasa ransa yayin gudanar da zanga-zanga a jihar Kano

0 243

An tabbatar da mutuwar Mutum guda yayin da magoya bayan gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ke gudanar da zanga-zanga bayanda kotun daukaka kara da yanke hukuncin korar nasarar da ya samu.

An bayyana sunan marigayin da Salisu Rabiu, wanda dan wasan kwallon kasa ne, na daga cikin wadanda ‘Yan sanda suka tarwatsa yayinda suke zanga-zanga.

Masu zanga-zangar na rike da alluna dauke rubutu kala-kala dake cewa a dawo mana da hakkin mu, mu Abba muka zaba, rashin adalci aka mana.

An ajiye jami’an ‘Yan sanda a mashigar jihar, inda masu zanga-zangar suka toshe hanyar katsina tare da hana matafiya wucewa.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar Abdullahi Kiyawa, ya fitar, ya tabbatar da mutuwar matashin dan karamar hukumar Fagge.

Wani safeton ‘Yan sanda ne yayi harbi yayin da ake gudanar da zanga-zangar ba tare da ya samu umarnin daga manyan su ba, lamarin da yayi sanadiyyar jikkatar mutane 2 da kuma mutuwar Mutum 1.

Kwamishin ‘Yan sandan Jihar CP Mohammed Gumel,Ya umarci kwamandan rundunar ‘Yan sanda na yankin Dala ACP Nuhu Digi domin gano dan sandan da yayi wannan aika-aika. Rundunar ‘Yan sandan Jihar ta yi takaicin rasuwar matashin, tare da taya ‘Yan uwa da Iyalan alhinin rasuwar sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: