Wani jigo a PDP ya roki Gwamna Elrufa’i daya sadaukar da albashin sa wajen karatu
Wani jigo a babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, Lawal Adamu Usman, ya roki gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, ya sadauƙar da albashinsa wajen ɗaukar nauyin karatun ɗalibai, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Wannan kiran yazo ne bayan gwamnatin jihar Kaduna ta kara kudin makaranta ga daliban dake karatu a makarantun gaba da sakandire mallakin jihar.
Da yake jawabi a wurin bada tallafin karatu da gidauniyar Lawal Adamu Usman ta yi ga dalibai 100 a Kaduna, jigon PDP ya yi kira ga gwamnan Kaduna ya zama shugaba abin koyi, ya sadaukar da kudin albashinsa wajen biyawa daliban kaduna kudin makaranta.