Abubakar Musa mai shekara 43 mazaunin Oshodi cikin jihar Legas yayi kutse cikin jerin rukunin motocin yan rakiyar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo.
Mai gabatar da kara mishozumu ya bayyanawa kotu cewa, mai laifin ya kutsa cikin jerin rukunin motocin ne a daren 19 ga watan Junairun da ta gabata, da misalign karfe 10 na dare, akan babban titin Oshodi zuwa Apapa a cikin birnin legas.
Mai shari’a Njuku ya rataya belin Naira 50,000 ga matukin, bisa saba dokar tuki ta sashen doka na 45 da sashe na 15. Musa ya nemi afuwar laifin akokarinsa na ayyana cewa tsautsayine ba ganganci ba.
Mai sharia Njoku ya dage karar zuwa 19 gawatan da muke ciki bayan sauraron uzurin direban