Wani dan takarar majalisar wakilai na PDP a mazabar Obi ya kubuta daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi

Dan takarar majalisar wakilai na jam’iyyar PDP a mazabar Obi, Moses Egbodo, ya kubuta daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi bayan sun karbi Naira miliyan uku a matsayin kudin fansa a ranar Asabar.
Dan takarar ya kubuta ne bayan kwanaki shida a hannun masu garkuwa da mutanen.
An yi garkuwa da shi ne tare da wasu mutane uku a cikin wata motar kasuwanci yayin da suke tafiya daga Makurdi zuwa Otukpo a ranar Litinin din data gabata.
Shugaban karamar hukumar Obi, Tony Akpa, wanda ya tabbatar da sakin ga manema labarai a Makurdi a jiya.
Ya ce, an sako mutumin ne a jiya da misalin karfe 7 na dare bayan ya shafe kwanaki shida a hannun masu garkuwa da shi.
Kakakin Rundunar Yan sandan Jihar Binuwai, SP Catherine Anene, ta ce basu samu labarin garkuwa da dan siyasar ba.