Wani ɗan sanda ya kashe wani ɗan jarida da bindiga a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Kongo
Wani ɗan jarida a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Kongo ya rasu sakamakon raunin da ya samu sakamakon harbinsa da bindiga da aka yi a lokacin da ƴan sanda suka yi arangama da yan bindiga a ƙasar.
Jean-Marie Luzingu na a Kinshasa a lokacin da aka samu arangamar.
Wani harsashi da wani ɗan sanda ya harba ne ya samu ɗan jaridar, kamar yadda wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana wa Mishapi Voice Radio.
Ƴan uwansa yan jarida dai na ci gaba da jimamin mutuwarsa a shafin Twitter.
A halin yanzu ana ci gaba da bibiya domin gano waɗanda suka haddasa wannan tarzomar.
Ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasar ta ce tana buƙatar a bi wa wanda aka kashe haƙƙinsa.
Asalin labarin: BBCHausa;