Wani Ɗan Majalisa Ya Ƙuduri Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Zamfara

0 446

Dan majalissar dake wakiltar mazabun Gusau da Tsafe a majalisar wakilai ta Najeriya Alhaji Kabiru Mai-palace yace zai yi duk wata mai iyuwa wajen samar da tsaro da kuma yaki da rashin aikin yi a mazabunsa.

Mai-palace wanda daya ne daga cikin ya’ayan jam’iyyar PDP mai adawa ya bayyana hakan ne ga manema labarai a garin Gusau.Ya ce shubannin gargajiya na daya daga cikin wadanda za su taka rawar gani wajen kawo karshen rashin tsaro dake addabar jihar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya rawaito cewa dan majalisar ya ziyarci wasu gidajen yada labarai a jihar, haka kuma ya bayyana cewa malaman addini da sauran yan siyasa da mahukunta na da rawar da za su taka kan al’amuran shugabanci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: