Wanda yayi tattakin nasarar Buhari ya rabauta da Mota da Miliyoyi

0 269

Gwamna Jihar Gombe Inuwa Yahaya ya gwangwaje mutumin nan da ya yi tattaki daga Gombe zuwa Abuja don murnar cin zaɓen Shugaba Buhari a 2015 kyautar mota.

Haka kuma BBC Hausa ta rawaito ce gwamnan ya bai wa Dahiru Buba Dukku kuɗi har naira miliyan biyu, kamar yadda yake ƙunshe cikin wata sanarwa da Ismal Uba Misilli mai bai wa gwamnan shawara kan kafafen yaɗa labarai ya fitar.

A baya mun kawo muku rahoton yadda Dahiru Buba mai shekara 50, yace yana fama da ciwon ƙafa sakamakon tattakin da yayi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: