Hukuma kula da jarabawa ta kasashen yammacin Afrika WAEC, ta rike sakamakon dalibai 262,803 da suka zana rubuta jarabawar ta wannan shekarar.
Shugaban ofishin hukumar Patrick Areghan, shine ya bayyana sakin sakamakon jarabawar a wani taron manema labarai.
Yace rike sakamakon jarabawar na da alaka da rahotannin satar amsa da aka samu.
A cewar sa,cikin adadin wanda suka yi jarabawar kashi 16.29 sune suka zauna domin rubuta jarabawar.
Ya kuma kara da cewa ana bincike dangane da rahotannin da aka samu na satar amsa kuma za’a gabatar da shi gaban kwamitin da hukumar ta kafa domin daukar mataki na karshe.
Ya kuma gargadi gwamnatotin da har yanzu basu biya hukumar kudin rijista ba cewa baza’a saki sakamakon daliban su ba, har sai sun biya.