Tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, ya bayyana ficewarsa daga zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar PDP.
Emeka Ihedioha ya bayyana janyewa daga takarar ne a wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar na kasa wanda kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito jiya a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labaran ya bayar da rahoton cewa, Emeka Ihedioha da sakataren jam’iyyar na kasa, Samuel Anyanwu ne kadai aka tantance a zaben fidda gwani na neman tikitin takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Imo.
A cikin wasikar, Emeka Ihedioha ya bayyana cewa ya cika shekaru 58 a ranar 24 ga watan Maris kuma yana da dalilin yin tunani a kan abubuwa da dama ciki har da makomar jihar da jam’iyyar PDP.
Tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai ya bayyana cewa kasancewarsa dan jam’iyyar tun kafa ta a shekarar 1998, ya amince da bukatar da jam’iyyar PDP reshen jihar Imo ta gabatar ga kwamitin gudanarwar jam’iyyar na kasa na neman yin sulhu wajen fitar da dan takarar gwamna.