Tsohon gwamnan Jigawa Dr. Sule Lamido yayi Allah wadai da kisan da akayiwa yan’uwa musulmai a birnin Jos dake jihar Plateau.
Wannan sanarwar na kunshe cikin sakon da mai magana da yawunsa Mansur Ahmad ya fitar, kuma aka rabawa manema labarai.
Inda yace Sule lamido a jiya ya ziyarci Sheikh Dahiru Usman Bauchi a gidansa dake Bauchi, inda ya jajantamasa bisa wannan babban rashin da yayi.
Haka kuma ya kwatanta kisan da akayiwa matafiyan akan hanyar Rukubu dake Jos a matsayin abin takaici.
Kafin hakan dai kamfanin dillacin labarai na kasa NAN ya bayar da rahoton cewa akalla musulmai matafiya 30 ne aka kashe a lokacin da suke dawowa daga ziyarar barka da Sabuwar shekarar musulunci da suka kai jihar Bauchi.
Sule lamido ya kuma jajatantawa iyalan wadanda suka rasa yan’uwansu, dama musulmai baki daya, tare dayin adduar Allah yajikansu da rahama.