Tsautsayi: Hatsarin Mota Ya Lakume Rayuwar Mutane 11

0 185

Kimanin mutane 11 ne suka mutu yayinda kuma 44 suka samu munanan raunika bayan hadarin mota daya auku a Jihar Ondo, tun bayan kakaba dokar kulle a jihar daga ranar 4 ga watan Afrilu zuwa 8 ga watan Mayu.

Jami’in hulda da Jama’a na hukumar lura da kiyaye dokokin tuki Jihar Ondo Mista Babatunde Akinbiyi shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

Mista Babatunde Akinbiyi, ya ce hadarin ya shafi motocin 41 ciki harda motocin gida 15 da motocin haya 11 da motocin kasuwanci 18 da babura 2 da sauran su.

Haka kuma ya kara da cewa fasinjojin 8 daga cikin wadanda akayi hadarin dasu sun mutu, sai kuma wasu fasinjoji 20 da suka munanan raunika  da kuma 13 da suka sami kananan raunika.

Kazalika ya kara da cewa cikin wadanda suka sami raunika 30 maza ne sai kuma Mata 14.

Leave a Reply

%d bloggers like this: