Tsaro: An sace wata Mata da Danta a Katsina

0 268

Wasu yan bindiga sun sace matar wani mutum mai suna Aliyu Mai-Yadi Charanchi tare da dansa dan shekara uku, a yankin karamar hukumar Charanci dake jihar Katsina.

Mazauna garin sun ce lamarin ya auku da misalin karfe 12 da rabi na ranar Talata.

An rawaito cewa yan bindigar sun tunkari gidan mutumin dake Unguwar Gabas a Charanchi.

Ba za a iya tabbatar da ko yan bindigar mahara ne ko wasu bata gari ne dake garkuwa da mutane domin samun kudin fansa ba.

Kakakin rundunar yansandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya kara da cewa har yanzu ana sauraron cikakken bayanin abinda ya faru daga baturen yan sanda na yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: