Tsarin bashin karatu ga ɗalibai wanda Shugaba Tinubu ya amince da shi zai fara nan ba da jimawa ba

0 257

Akalla matasa miliyan 1.2 ne za su fara cin gajiyar shirin bai wa ɗalibai bashin karatu da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ɓullo da shi.

Ana sa ran tsarin shiga cikin shirin, wanda Shugaba Tinubu ya amince da shi a ranar 3 ga Afrilu, zai fara “nan ba da jimawa ba,” kamar yadda Akintunde Sawyer, Manajan Darakta da kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Asusun ba da bashi na Ilimi na Najeriya ya bayyana.

A ƙarkashin wannan shiri, kashi ɗaya cikin dari na kuɗaden shiga na shekara-shekara na Hukumar Tara Haraji ta Kasa zai ɗauki nauyin shirin.

Sharuɗɗan biyan bashin sun nuna cewa za a fara biyan bashin shekaru biyu bayan kammala aikin yi wa kasa hidima, NYSC.

Sawyer ya zayyana tsarin rajistar, wanda ya nuna cewa wadanda za su ci gajiyar shirin za su bukaci bayar da lambar jarabawarsu ta JAMB, da Lambar Shaida ta Kasa, NIN, da Lambar Tabbatar da Banki, BVN, don neman rancen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: