Tinubu zai kai ziyarar aiki Faransa

0 79

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Najeriya a ranar Laraba domin kai ziyarar aiki Faransa, inda zai yi kusan makonni biyu.

Haka na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga.

Shugaban ya ce zai yi amfani da lokacin ziyarar don yin nazari kan yadda gwamnatinsa ta kasance a yayin da ta ke gab da cika rabin zango.

Haka kuma zai duba manyan nasarorin da gwamnatin ta samu tare da duba garonbawul ɗin da ya yi da gaggauta ci gaban da ya ke so a samu a shekara da ke tafe.

Sanarwar ta bugi ƙirji da nasarar da ta ce gwamnatinsa ta samu a fannin tattalin arziki, inda ta bayar da misali da bunƙasar asusun ajiyar kuɗaɗen waje da babban bankin ƙasar ya ce ya kai $23.11 biliyan.

Idan aka kwatanta da $3.99 biliyan da suka ce sun tarar a shekarar 2023.

Shugaban ya bayyyana cewa zai ci gaba da jagorantar al’amuran gwamnatin Najeriya, a yayin da yake Paris.

Leave a Reply