Tinubu ya yi wata ganawar sirri da takwaransa na Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa

0 197

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ya yi wata ganawar sirri da takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, a birnin Johannesburg, yau Alhamis.

A tattaunawar da suka yi kafin ganawar ta sirri a birnin wanda shi ne mafi girma a Afirka ta Kudu Shugaba Ramaphosa ya gode wa Shugaba Tinubu kan yadda ya halarci bikin sake rantsar da shi, shugaban kasa a wa’adi na biyu wanda aka yi jiya Laraba.

A yayin ganawar Tinubu ya sheda wa Ramaphosa cewa bayanan da jawabin Ramaphosa na lokacin rantsuwar kama aiki ya tabo yawancin matsalolin da kasashen Afirka suke fuskanta, kuma ya nuna cewa akwai bukatar shugabanni su hada kai domin samar da mafita. A ranar Juma’a 14 ga watan Yuni ne aka sake zaben Mista ramaphosa a matsayin shugaban kasar a wa’adi na biyu na tsawon shekara biyar, bayan yarjejeniyar da jam’iyyarsa ta ANC ta kulla da Democratic Alliance.

Leave a Reply

%d bloggers like this: