Tinubu ya yi kira da a gaggauta kawo karshen takaddamar da ke tsakanin Najeriya da Dubai

0 353

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a gaggauta kawo karshen takaddamar da ke tsakanin kasar da Hadaddiyar Daular Larabawa, da ya shafi zirga-zirgar jiragen sama da bayar da biza tsakanin kasashen biyu.

Tinubu ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin Jakadan Hadaddiyar Daular Larabawa a Najeriya, Salem Saeed Al-Shamsi a fadarsa da ke Abuja.

A shekarar da ta gabata, Hadaddiyar Daular Larabawa ta dakatar da bayar da biza ga ‘yan Najeriya, bayan da kamfanin jiragen sama na Emirates ya dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Najeriya saboda takunkumin da aka yi wa wasu kasashen waje.

Kamfanin ya ce ya dauki matakin ne bayan duk kokarin da ya yi na magance matsalar da hukumomin Najeriya ta hanyar ka’ida ya ci tura. Shugaba Tinubu ya ce ya kamata a gaggauta magance matsalar, yana mai cewa a shirye yake ya sa baki don kawo karshen matsalar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: